Da Duminta: Likitoci Sun Dakatar Yajin Aiki

Kungiyar likitoci na Najeriya ta bayyana cewa ta dakatar da yajin aiki daga ranar Linitin 22 fa watan Yuni 2020.

likitocin wadanda suka shiga yajin aiki a ranar Litinin 15 ga watan Yuni wanda yajin aiki na makonni biyu ne. kungiyar ta yanke hukuncin yin hakan ne bayan zaman da ta gudanar da gwamnatin tarayya


Duk da haka dai kungiyar ta sanar da dakatar da yajin aikin kafin mako daya da yin yajin.

Kungiyar NARD ta bayyana hakan ne a wani sanarwa da ta fitarwa manema labarai wanda ya samu rattafa hannun Shugaban kungiyar, Dakta Aliyu Sokomba a ranar Lahadi , 21 fa watan Yuni 2020 a birnin tarayya Abuja bayan mambobin kungiyar 300 sun halarci zaman majalisar zartarwa na kasa.

Kungiyar ta dakatar da yajin aikin ne domin ya baiwa gwamnati lokacin cika alkawarin da ta yi ma ta biyo bayan bukatun da kakakin majalisar wakilai yayi, Femi Ghajabiamila, ya mikawa sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya da masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *