Da Duminta: Jam’iyyar APC Ta Dakatar Da Sakatarenta Na Kasa Victor Giadom

Jam’iyyar APC reshen jahar Ribas ya dakatar da sakataren jam’iyyar ta kasa Victor Giadom daga jam’iyyar


Mai baiwa shugaban jam’iyyar mai rikon kwarya Igo Aguma, shawara a kan harkokin da suka shafi yada labarai, Livingston Wechie, ya ce jam’iyyar ta yanke hukuncin hakan ne sakamakon raba kan jam’iyyar da Giadom yayi a jam’iyyar ta kasa bayan kwamitin gudanar da bincike a kan lamarin ga gama gudanar da binciken ta tare da bada rahoto.

Wechie said; 

”Kwamitin ta bada umurnin dakatar daga jam’iyyar tare da duk wasu abubuwan Da ya shafi jam’iyyar sakamakon raba kan jam’iyyar da Giadom yayi a jam’iyyar ta kasa wanda Ya Janyo rikici a jam’iyyar

”Saboda haka Victor Giadom ba tare da bata lokaci ba, ya ruwaito wasikar neman gafara ga Jam’iyyar sannan kuma ya wallafa wasikar a jaridu dake kasar nan.

”Rahoton kwamitin an mika ta zuwa Shugaban majalisar zartarwa na jam’iyyar na jahar sannan an amince da hukuncin da kwamitin ya yanke

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *