Bayanin Zaman Sirrin Da Buhari Ya Yi Da Lawan A Ranar Lahadi

Shugaban majalisar Dattijai, Ahmad Lawan, ya bayyaan bayanin zaman da Yayi da shugaba Muhammadu Buhari

Shugabannin sun gudanar da zaman a sirrance a ranar Lahadi a fadar Shugaban kasa dake Abuja.


Buhari da lawan sun yi magana a kan abubuwar da ke gudanar a kan kasar musamman a kan harkar tsaro Tare Da rikicin jam’iyyar APC da sauransu

a yayin da yake magana da manema labarai Lawan ya ce “ sanin kowa ne kasar nan na fuskantar matsalar tsaro sosai hakan ya sa na zo na yi zama Da Shugaban kasar nan Domin Na tattauna Da shi a kan abunda mu tattauna a Sauran yan majalisar dattijai Domin bin hanyar da ya kamata wajen kawo karshen tsaro a kasar nan.

Shugaban Majalisar Yayi kira ya Sojojin Kasa, da sojojin sama, da Sojojin ruwa, da ‘yan sanda, Tare Da hukumar kula Da migeration Da su yi dauka ma’aikata


A bangaren cutar Korona kuma, ya kara cewa: “An ware naira biliyan N500 sakamakon cutar korona a sabuwar kasafin kudin bana Don tallafawa ma’aikatu, su CBN, NNPC da IOCs su bada gudunmawar kayayyakin abinci Don tallafawa talakawa a wannan lokaci na korona.”

A cikin makon nan, Shugaba buhari ya gargadi hafsoshin tsaro inda ya ce ba zai so ya kara jin wani zance daban daga wurin su ba yayin da ya ce su kara hazaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *