An Gano Makamai masu yawan gaske A Gidajen Wani Dan Majalisar Jihar Zamfara

Al’ummar garin Gusau babban birnin jihar Zamfara sun yi matukar cika da mamaki sakamakon gano makamai da jami’an tsaro suka yi a gidan wani dan majalisar jihar, wanda aka sakaye sunansa. Bayan da labarin lamarin ya yadu a birnin na Gusau da makwabciyarta garin Tsafe, mazauna yankin sun shiga cikin fargaba da ban mamaki.

Kamar yadda majiyarmu ta bayyana, an gano makaman ne sakamakon wasu mutane da aka kama da makamai a jihar Kano da suka bayyana cewa a gidan dan majalisar na jihar Zamfara suke ajiye makamansu.

“Mun gano cewa sakamakon wannan rahoton ne ya sa jami’an tsaro yin tattaki zuwa gidajen dan majalisar da ke garin Tsafe da Takama a birnin Gusau”, kamar yadda majiyar ta bayyana. Majiyar ta kuma kara da cewa, bindigogi kirar AK47, akwatinan harsashai da barkonon tsohuwa suna daga cikin makaman da aka gano a gidan dan majalisar da ke Gusau, yayin da kuma aka samu gurnet a gidansa da ke Tsafe.

A yayin jin tabakin mai magana da yawun ‘yan sandan jihar ta Zamfara, DSP Lawal Abdullahi game da lamarin, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce jami’an tsaron da sukayi binciken ne suka bayar da rahoton kuma ya ce babu abin da zai kara fiye da haka akan lamarin

Madogara: Hausa Online TVs.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *