‘Yan Bindiga Fiye Da 600 Zaune A Tsaunin Zangang A Jahar Kaduna – Matasa Suka Fadawa Hukumomin TsaroKungiyar matasan Kaura Tare Da kungiyar matasa Takad na kasa a ranar Asabar sun fadawa hukumomin tsaro cewa da su yi kokarin tararrasa sansanin ‘yan bindiga da ke saunin Zangang a karamar hukumar Kaura .

kungiyiyon sun bayyana hakan ne a Wata sanarwa da suka fitar wanda ya samu sa hannun shugabannin kungiyoyin Derek Christopher da Abun Vincent a Kafanchan.


kungiyoyin sun bayyana cewa tsaunin ya kasance kamar gida ga ‘yan bindiga inda suka bayyana akalla ‘yan bindiga 600 ke zama a wurin.

sun yi kira ga Hukumomin tsaro da su “kara hazaka wajen lallasa’yan ta’adda tare da lalata wurin buyan nasu da ke saman saunin Zangang, inda ‘yan bindiga sama da 600 Masu dauke da manyan makamai ke buya a Tsaunin

A Sanarwan sun gargadi cewa a nan ne a ke kashe ‘yan Takad, da Fulani tare da yan kabilar Sholio musamman da kisan da ya faru a cikin ‘yan kwanakin nan da suka gabata a Zangang da Addu”.

a cewarsu, dalilin da yasa ‘yan bindigar ke kai harin shine saboda albarkatun kasa dake binne a kasan yankin

matasan sun yi Allah wadai da abunda’yan bindigar ke yi a yankinsu inda suka bayyana cewa hakar albarkatun kasa na karfin Tin ba a bisa kaida ya kasance abun yi a yankin


“Akwai hakar albarkatun kasa na karfin Tin dake faruwa a yankin wanda yan kabilar Ganawuri ke yi; Suna sayar da albarkatun da suka haka a jahar Filato ne.”

MutaDuk da haka, hukumomin tsaro a yankin sun cafke wasu mutane 2 ‘yan Ganawuri tare da wasu Fulani ‘yan bindiga 3 a kan zargin cire rufin gidaje dake Zangang.


Matasa sun bukaci ‘yan sanda a Kaura da su dau gagarumin mataki game da hakan domin tabbatar da cewa sun cafke wadannan mutanen da suka addabi wannan yankin.

Sanarwa ya yi kira ga gwamnatin jahar Kaduna dasu kara yawan ofishin ‘yan sanda dake yankin Saboda yawan ‘yan bindiga da ke Kudancin jahar Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *