Saura Kadan Mu Kawo Karshen Cutar Korona A Kano – Gwamna Ganduje

Gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce Gwamnatin sa na samun nasara wajen yaki da cutar corona duba da yadda sakamakon gwajin cutar ke fitowa.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakanne yau a dakin taro na coronation yayin taron horar da yan jaridu da suka fito da ga kafafan yada labarai daban daban na jahar nan kan wayar da kan alumma kan cutar corona wanda Gwamnatin jahar Kano hadin guiwa da Kano Against Covid19 suka shirya .

Ganduje yace koda a Wannann makonan anyi gwajin cutar ta korona na mutane 2,603 wanda sakamakon gwajin mutane 140 ne ya nuna suna dauke da cutar ta korona, inda ya ce wannan nasara ce dake nuna cewa Gwamnatin na cin nasara a yaki da cutar .Da yake jawabi jagoran kungiyar dake yaki da cutar corona ta kano Against Covid19 Professor Muhammad Tabi,u San ya hori yan jaridun dasu mayar da hankali wajen fadakar da jammaa kan yakar cutar ta Covid19.A nasa ɓangaren kwamishinan yada labarai aladu na jihar Kano, Muhammad Garba ya ce an shirya taron ne domin Kara dankon zumunci tsakanin yan jaridu da Gwamnatin da kuma horar da su kan yadda zasu dafawa Gwamnatin wajen wayar da kan alumma kan yadda zasuyi amfani da dokokin masana harkokin lafiya domin Kare kansu daga cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *