Mutum 6 Sun Mutu, Gidaje 600 Sun Rushe Bayan Ruwan Sama Da Iska Mai Karfi A Kano

Dailytrust ta rawaito cewa mutum shida suka rasa rayukansu baya ga gidaje 600 da suka rushe sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da iska mai karfi a kananan hukumomi hudu a jihar Kano.

Kazalika wasu mutum 1,752 sun rasa muhallansu sakamakon iftila’in a cikin mako guda a jihar, inji Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano.Shugaban hukumar Sani Jili ya ce wutar lantarki ta kashe daya daga cikin mamatan, sauran biyar din kuma gini ne ya fada a kansu.

Sani Jili ya ce iftila’in ya shafi Kananan Hukumomin Gwale, Gwarzo Rimin Gado, da kuma Kibiya ne a cikin a makon jiya.

Ya ce hukumarsa na jiran rahoton sauran kanana hukumomin da abin ya shafa yayin da ma’aikata ke kokarin tattara alkaluman barnar da aka samu.

A cewarsa Rimin Gado da Kibiya sun riga sun gabatar da rahotanninsu, har an tallafa musu da kayan rage radadi a matakin farko ga wadanda suka yi asara.

Kaya da aka rabawa mutanen kai tsaye sun hada da “kayan abinci, tufafi da kayan shinfida, sai kuma buhunan siminti”, inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *