Matashi Ya Yiwa Nakasassa ‘Yar Shekaru 15 Fyade A Jigawa

‘Yan sanda sun cafke wani matashi dan shekaru 34 a Duniya wanda aka bayyana da sunar Samson Eze a kan zargin yiwa wata nakasassa ‘yar shekaru 15, Fatima Aliyu, fyade a karamar hukumar Gwaram dake jahar Jigawa

Kakakin rundunar ‘yan sanda reshen jihar Jigawa, SP Abdu Jinjiri ya tabbatarwa manema labarai da haka.

Ya bayyanawa manema labarai cewa an mikawa ‘yan sanda dake karamar hukumar Gwaram cewa Samson Eze ya yiwa yar shekaru 15 fyade a yankin. ” A ranar 20/05/2020 ‘yan sanda a karamar hukumar Gwaram an kawo masu karar wani matashi dan shekaru 34, Samson Eze, mazaunin kwatas din Galambi a karamar hukumar Gwaram ya kira wata matashiya nakasassa ‘yar shekaru 15 wacce ita ma ta kasance mai zama a wannan yankin ya ma ta fyade

“Da samun labarin hakan, ‘yan sanda suka cafke wanda ake zargi sannan kuma aka garzaya da ita yarinyar da aka yiwa fyade zuwa asibiti domin duba lafiyar jikinta.”

Ya ce a yayin da ‘yan sanda suke gudanar da binciken su a kan lamarin sun gano cewa matashin ya taba jima’i da yarinyar har sau 2 ba tare da amincewarta ba.

Haka zalika shi ya sa ‘yan sanda basu mika karar fyade ba a kan matashi sakamakon ma’anar fyade na sashi 283 na panel code na Arewacin Najeriya

.

Shi duk da haka ya bayyana cewa wanda ake zargi an caje shi da aikata laifin karya dokar lalata kamar yadda sashin 285 na wannan code din.

Bincike na manema labarai ya bayyana cewa ‘yan sanda na kokarin rufe karar domin kare wanda ake zargi. Kakakin ‘yan sandan, duk da haka ya karyata hakan inda ya cewa ‘yan sanda suna aiki da dokar kasa ne na sashi 283 da kuma 285 na panel code na Arewacin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *