Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Mutumin Da Ya Lalata Budurcin ‘Yar Makwabtarsa ‘Yar Shekara 9 Ta Hanyar Fyade

Wata babban kotu dake jahar Legas ta yi watsi da karar da aka mika ma ta a kan wani mutum da ya lalata budurcin ‘yar makwancinsa ta hanyar yi ma ta fyade

Wannan karar da aka yi watsi da shi ya kai shekaru 5 ana sauraransa wanda ake zargin wani mutum, Niyi Oyelami, da lalata budurcin ‘yar makwabcinsa ta hanyar yi ma ta fyade kafin mai sharia, Jutsic Oluwatoyin Ipaye na babbar kotun Legas mai gudanar da zamanta a Ogbosere ta yi watsi da karar.

Kotu ta wanke Oyelami a kan zargin da ake zarginsa da aikata bayan shekaru 5 da zaman a kan karar.

A yayin da alkalin kotun ke yanke hukuncin ya ce wadanda suka mika karar basu da tantaccen shaida da ya nuna shi wanda ake zargi ya aikata wannan laifin

Ya ce shaidun suka shaida faruwar hakan na wadanda mika karar zuwa kotu sun kasa bayyana lallai wanda ake zargi ya aikata laifin da ake zarginsa da shi.

Ta ce, “Niyi Oyelami, sakamakon hakan kotu ta wanke ka daga zargin da ake ma ka na lalata budurcin ‘yar shekaru 9 wanda aka mikawa wannan kotun a ranar 27 ga watan Nuwamba 2015.”

A yayin da kotun ke saurarar karar lauyar da ta mika karar zuwa kotu Ms Bisi Bello ta fadawa kotun cewa shi wanda ake zargi ya aikata laifin ne a ranar 2 ga watan Mayu 2015 a yankin Agbule Egba dake birnin Legas. Ta ce shi wanda ake zargi ya lalata budurcin yarinyar ‘yar shekaru 9 wacce ta kasance yar makwabtansa tare da yi ma ta fyade inda ta ce hakan ya sabawa sashi 137 na dokar jahar Legas 2011.

Lauyar da ta mika karar zuwa kotu ta gabatar da shaidu 3 a gaban kotu kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *