Kotu Ta Dakatar Da Sabon Shugaban APC Na Ƙasa Daga Shugabancin Jam’iyyar

A ranar Juma’a ne wata Babbar Kotun Jihar Ribas dake zamanta a Fatakwal, jihar Ribas, ta dakatar da tsohon Mataimakin Sakataren Jam’iyyar APC na Ƙasa, Victor Giadom daga ɗaukar kansa a matsayin Shugaban APC na Ƙasa.

Kotun da Mai Shari’a Florence Fiberesima ya jagoranta, a wata ƙara da Dele Moses da sauransu suka shigar ta kuma bada umarni na din-din-din da ya hana Mista Giadom ɗaukar kansa a matsayin mamba na Kwamitin Zartarwa na Ƙasa na APC, NWC.

A cewar Mai Shari’a Fiberesima, Mista Giadom ba zai iya iƙirarin zama mamba na NWC ba, bayan ya yi murabus daga muƙaminsa don yin takara a zaɓukan 2019 a matsayin Mataimakin Gwmana.

Kotun ta kuma hana Mista Giadom fitar da, sa hannu ko aika kowace irin takarda zuwa ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ko kuma wata hukuma a matsayin Shugaban APC na Ƙasa ko Muƙaddashin Shugaban APC ko wani muƙami a matsayin jami’in APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *