Kashe-kashen Arewa: Ba Komai Ya Janyo Hakan Ba Face Sabawa Allah Da Al’umma Ke Yawan Yi – Sheikh Bichi

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano na kungiyar Izala, Sheikh Sani Sharif Umar Bichi ya ce ‘yan Arewa su suka jawowa kan su kashe-kashen da ake yi musu a sakamakon rashin bin shari’ar musulunci da sabawa Allah .

Sheikh Bichi ya kara da cewa “Arewa yanki ne na musulunci kuma mun yi wa Allah alkawarin bin dokokinsa kuma muka saba masa. ‘Yan Arewa sune gwanayen zina, su ne gwanayen luwadi, madigo da sauran alfasha iri-iri.

Sheikh Bichi ya kara bada misali ya ce “gaba daya shugabannin tsaro ‘yan Arewa ne, shugaban kasa dan arewa ne kuma jami’an tsaron da suke a arewa babu a kudu. Dan haka mun tsokano Allah ne shi ya sa ya jaraba mu”.

Sannan ya ce “wannan bala’in ya fi karfin Buhari kuma ya fi karfin jami’an tsaro. Mafita ita ce mu tuba zuwa ga Allah, sai Allah ya yafe mana.

“Shugaba Buhari mutumin kirki ne kuma yana iya bakin kokarin sa akai, ba shi yake fashikanci ba”.

Sheikh Sharif Bichi ya yi wannan jawabin ne a wa’azin bayan sallar Juma’a da yake yi duk sati kamar yadda ya saba gudanarwa a masallacinsa dake Bichi a jihar Kano.

Daga karshe ya yi addu’o’i ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kasar mu da jiharmu da ma Musulman duniya baki daya.

Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *