Karanta Amfani Gawayi Guda 10 Da Ba Ka Taba Sani Ba

Jama’a da dama musamman a arewacin Nijeriya suna ganin amfanin gawayi bai wuce a saka a cikin dutsen guga ba, ko kuma a cikin kasko domin yin girki ko turaren wuta, ko a dumama daki lokacin sanyi.

Bincike dai ya nuna cewa bayan wadannan alfanun da gawayi ke yi, yana kuma da wasu amfani wajen gyara lafiyar jiki wanda bai kamata mu yi watsi dasu a gidajenmu ba.

Kadan daga cikin amfanin da gawayi ke yi na kamar haka

1) Yana da amfani wajen tsaftace gida da kuma warin jiki misali, idan wani lungu a gida yana wasu, za a iya sanya Gawayi a wurin, in kuwa jiki ne, sai a yi garin gawayin, an sanya a jiki.

2) Gawayi na hana kayan marmari lalacewa, abin da za a yi kawai shi ne a dama gawayin sai a tsoma kayan marmarin a ciki

3) Gawayi na taimakawa wajen cire sinadiran da ke da lahani daga cikin kayan abinci. Za a tsoma kayan marmarin cikin ruwan Gawayi

4) Gawayi na sanya hakora su yi haske idan aka yi amfani da shi wajen goge hakoran.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *