Kano: Tun Da An Buɗe Gidajen Kallo A Buɗe Makarantun Islamiyya – Sheikh Gadon Ƙaya

Babban malamin addinin musulunci Sheik Abdallah Usman Gadon Kaya, ya bayyana cewa ya kamata Gwamnatin Kano ta bude makarantun Islamiyyu domin yara su koma makarantu domin su kara ninka addu’o’i na rabuwa da cutar Corona virus.

Malamin ya bayyana haka ne yayin tattaunawar sa da gidan Radio Dala FM Kano a jiya Juma’a.

Ya ce ” Bude makarantun Islamiyyar zai taimaka matuka musamman ma wajen kara rubanya addu’ar da a ke na Allah ya kawar da cutar”.

Ya ce tun da gwamnatin Kano ta bude gidajen kallon kwallo a Kano, babu kamata ya yi su ma makarantun Islamiyya a ba su dama su bude domin ci gaba da karatun su.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara kaimi wajen dakile yawaitar kashe-kashen al’umma da ‘yan bindiga su ke yi a Arewacin Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *