COVID-19: Da Yiwuwar Gwamnati Za Ta Rage Yawan Kudaden Da Manyan Jami’an Gwamnati Ke Dauka

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa ya kamata a sake zama a tattauna irin kudaden da ake bannatarwa akan manyan jami’an gwamnati a kasar nan.

Ya ce abin na da wuya saboda wadanda zasu yi gyaran na amfana da yanayin; amma dai wajibi ne a san na yi.

Osinbajo ya bayyana hakan ne yayinda yake amsa tambayoyin tsohon gwamnan bankin CBN kuma tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, a taron yanar gizon da Cocin Emmanuel ta shirya kan tattalin arzikin Najeriya idan COVID-19 ta gushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *