An Kama Matasan Da Suka Dauki Bidiyon Wata ‘Yar Shekaru 12 Yayin Da Suke Ma Ta Fyade

Rundunar ‘yan sanda reshen jahar Anambra ta ce ta cafke wasu matasa biyu a kan zargin daukar bidiyon wata yarinya a yayin da daya daga cikinsu ke ma ta fyadea kauyen Ozubulu da ke karkashin karamar hukumar Ekwusigo a jahar.

Kakakin rundunar na jahar, Haruna Mohammed, ya bayyana hakan ga manema labarai a wani sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a 19 ga watan Yuni, inda ya ce shi wanda ake zargi Sunday Akanigbo (dan shekaru 30) ya yiwa wata yarinya fyade a yayin da wani abokinsa, Ikemefuna Muoma (dan shekaru 28) ke daukar yadda fyaden ke gudana.

Haruna said both men have confessed to the crime and would be charged to court soon.

Haruna ya ce duk wadanda ake zargi sun furta aikata zarginsu da ake yi sannan za a caje su zuwa kotu nan bada dadewa ba.

“A ranar 18/06/2020 da misalin karfe 1:45, ‘yan sanda dake aiki a ofishin ‘yan sanda dake Ozubulu sun cafke wani matashi dan shekaru 30, Sunday Akanigbo dake Amakwa Ozubulu dake karkashin karamar hukumar Ekwusigo a jahar Anambra.

Shi wanda ake zargi a watan Afrilu ya lalata budurcin wata yarinya ‘yar shekaru 12 a yayin da abokinsa Ikemefuna Muoma (dan shekaru 28) ya dauki bidiyon fyaden.

Hakazalika, su wadanda ake zargi sun furta aikata laifin sannan kuma mun samu karbar bidiyon a hannun wadanda ake zargi. Inda abun ya faru ya samu ziyartar ‘yan sanda domin gudanar da bincike a kan laarin sannan kuma ita wacce aka yiwa fyaden an tafi da ita zuwa asibiti domin duba lafiyarta.

Kwamishinan ‘yan sanda na jahar, CP John B. Abang, fdc ya bada umurnin mika karar zuwa sashen gudanar da bincike na ‘yan sanda (CID) da ke Awkwa don gudanar da takamammen bincike a kan lamarin bayan hakan ne za a caje su wadanda ake zargi zuwa kotu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *