Allah Ya Yiwa Mataimakin Shugaban BUK Ya Rasuwa

Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano, BUK, Ɓangaren Gudanarwa, Farfesa Haruna Wakili ya rasu yana da shekaru 60.

Majiyarmu ta rawaito cewa marigayin, wanda Farfesan Tarihi ne, ya rasu a Babban Asibitin Ƙasa dake Abuja, bayan ya sha fama da cutar kansa.

Da yake tabbatar da rasuwar tasa, Mataimakin Shugaban BUK, Ɓangaren Karatu, Adamu Idris Tanko, ya ce za a binne marigayin ne a mahaifarsa, Haɗeja dake jihar Jigawa.

Farfesa Tanko, wanda Farfesan Labarin Ƙasa ne, ya ce an kai marigayin Indiya don samun kulawa kimanin watanni shida da suka wuce, an kuma dawo da shi gida a lokacin da aka kafa dokar kulle ta COVID-19.Adnairax

Mista Wakili, wanda ya ƙware a Tarihin Zanga-zanga, Juyin Juya Hali, Rikice-rikice, Nazarin Zaman Lafiya, Dimokuraɗiyya da Kyakkyawan Shugabanci, shi ne tsohon Darakatan Cibiyar Bincike da Bada Horo Kan Harkokin Dimokuraɗiyya dake Mambayya House, kuma Kwamishinan Ilimi a Jigawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *