Zaɓen 2023 Ke Gaban ‘Yan Siyasa Ba Kisan Jama’a Ba – Dalung

Zaben 2023 Ne A Gaban ‘Yan Siyasarmu Ba Wai Kisan Da Ake Yi Wa Mutane Ba, Saboda Ko Ba Jama’a Za Su Yi Wa Kansu Aringizon Kuri’u Su Ci Zabe, Cewar Tsohon Minista Solomon Dalung

A Bidiyon da Mista Dalung ya bayyana haka, ya kara da cewa tunda ake wannan kashe-kashen babu wani gwamna da ya hada zama da Sarakuna, Malamai, Fastoci, tsoffin da matasa domin tattaunawa akan tabarbarewar tsaro.

A baya can dai tsohon ministan ya kasance na hannun daman shugaba Buhari kafin shugaban ya ajiye shi bayan lashe zaɓen shekarar 2019.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *