Tabarbarewa Tsaro: Ban Gamsu Da Rawar Da Ku Ke Takawa Wajen Yaki Da Ta’addanci – Buhari Zuwa Ga Hafsoshin Tsaro

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya shaidawa manyan hafsoshin tsaron kasar nan cewar bai gamsu da rawar da suke takawa wajen tinkarar matsalolin tsaron da suka yiwa kasar nan dabaibayi ba.

Bayan ganawar da Buhari ya yi da su a fadar sa, mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno yace shugaban ƙasar ya sake bayyana damuwar sa kan halin da kasar ke ciki.

Buhari ya ce shawo kan matsalar tsaro na daya daga cikin alkawuran da ya yiwa al’ummar ƙasar nan, bayan farfado da tattalin arzikin kasar nan da kuma yaki da cin hanci da rashawa, amma samun nasara akan guda biyu ba tare da samar da tsaro ba zai zama aikin banza.

Monguno yace Buhari ya shaidawa hafsoshin cewar ba zai amince da cigaba da samun tabarbarewar tsaro a kasar ba, domin kuwa babu wanda ya tilasta masa nada su a mukamin.

Mai bayar da shawarar ya ce shugaban kasa ya shaidawa hafsoshin cewar al’amura na hannun su wajen sauke nauyin dake kan su na shawo kan matsalar tsaron da hana yaduwar makamai da kuma safarar miyagun kwayoyi.

Harkoki tsaro sun sake tabarbarewa a ƙasar nan sakamakon karuwar hare haren mayakan book haram a arewa maso gabas da kuma Yan bindiga a arewa maso yamma, abinda yayi sanadiyar salwantar rayukan dimbin jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *