Mahaifiya Ta Aika Danta Lahira Ta Hanyar Yi Masa Dukan Tsiya

Wata mata da ke zama Agbarha dake kudancin Warri, ta yiwa danta dan shekaru 7 dukan tsira har lahira

Yaron ya rasu ne a ranar Litinin da daddare bayan ta masa duka har sai da yayi suma. inji wadanda suka shaida faruwa abun suka ce;

“Mahaifiyar ta hora yaron a yayin da ta ce masa ya tuja babur wato ya zauna a bisa kan isak amma yaron da kuzarin yin hakan saboba bai ci abinci ba. Hakan ya sa ta ta fusata har ya kai ga ta masa duka wanda hakan ya sa shi suma kafin ya mutu”

Rundunar ‘yan sanda reshen jahar Delta ta tabbatar mana da faruwan hakan kuma ta ce ta kama mahaifiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *