Mace ta shiryawa ƙawarta gadar zare; ta sa mazaje 8 majiya ƙarfi sun yi mata fyaɗe a Adamawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta cafke wata mata mai shekaru 30 da haihuwa mai suna Zainab Jafaru bisa zargin shiryawa aminiyarta gadar zare ta hanyar hada baki da wasu maza su 8 don su yi wa aminiyarta mai shekaru 33 fyade a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Zainab ta yaudari kawar tata ne ta hanyar gayyatarta don ta raka ta zuwa ganin saurayinta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje, ya bayyana cewa Zainab ta dauki aminiyarta ta kuma mikata ga wasu maza su 8 a dabarance, inda su kuma suka yi mata fyade bayan Zainab din ta bace daga inda ta kai aminiyar tata.

Lamarin dai ya faru ne a ranar 12 ga wannan wata na Yuni a kauyen Gerio cikin yakin Jambutu a karamar hukuma Yola ta arewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *