Laifukan Fyade 42 Aka Tura Kotu A Watanni 6 – Hukumar ‘Yan Sandar Kano

Hukumar ‘yan sanda reshen jihar Kano, tace ta tura laifukan fyade guda 42 zuwa kotu daban-daban a cikin watanni 6 a jihar, daga watan Janairu zuwa 13 ga watan Yuni da muke ciki.

Mai magana da yawun hukumar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana manema labarai a Kano, a ranar Alhamis, inda bayyana cewa wanda lamarin ya ritsa da su ‘yan mata da manyan mata, an sallame su daga cibiyoyin lafiya bayan da aka tabbatar da samuwar lafiyarsu.

Ya bayyana cewa da yawa daga cikin laifukan an aikata su a gine-ginen da ba a kammala su ba.

Kamar yadda ya bayyana a wani bincike da hedkwatar hukumar ta gudanar “kaso 33.3 daga cikin laifukan an aikata su ne a gine-ginen da ba a kammala ba, sai kuma kaso 17.7 da kuma aka aikata su a gonaki.

Kiyawa ya kara da cewa “kaso 15.6 na laifukan an aikata su ne a gidajen wanda lamarin ya afkawa, sai kaso 6.7 a gidajen wanda suke aikata laifin”.

Jami’im ya yi kira ga iyayen yara da sa ido sosai, saboda gudun mugaye da zasu bata musu yara.

Sannan ya kara jan hankalin al’ummar jihar Kano da suke kai rahoton dukkanin wani laifi sa ya shafi fyade ga caji-ofis mafi kusa da su.

A kwanakin da suka gabata ne Najeriya ta tsinci kanta cikin muggan laifukan fyade wanda da an aikata sai a kashe matan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *