Dan Achaba Ya Yiwa ‘Yar Shekaru 6 Fyade Har Sau 2

Wani dan achaba dan shekaru 28 a Duniya ya shiga hannu a yayin da ake zarginsa da ya yiwa yar shekaru 9 fyadd har sau 2 a kauyen Idye da ke birnin Makurdi a jahar Benuwe
 

Shi wanda ake zargin sunansa Terver Awuba ya kasance ana zarginsa da yiwa yar shekara 6 fyade sau 2. Shi wanda ake zargi ya ja yarinya zuwa dakin a yayin da mahaifiyarta ta aike ta zuwa sayen indomie a ranar 3 ga watan Yuni 2020 da misalin karfe 7:30 na dare.

Dan achaban ya sake aikatawa yarinyar fyade a ranar 5 ga watan Yuni 2020 da misalin karfe 2:00 na rana inda ya baiwa yarinyar naira N100. An cafke Terver bayan ya aikata fyaden na 2 wanda hakan ya sabawa sashi 284 na dokar jahar Benuwe 2003 bayan mahaifiyar ta mika kara.
 

Majistare Isaac Ajim ya bada umurnin garkame dan achaban sannan ya daga saurarar karar zuwa 28 ga watan Agusta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *