An Cafƙe Matashin Da Ya Yi Barazanar Kashe Buhari Da Gwamnan Gombe

Wani matashi mai shekaru 30 da haihuwa ɗan kabilar Fulani da ya ke da mata da ‘ya’ya uku mai suna Usman Muhammad dan asalin garin Bambam a karamar hukumar Balanga ta jihar Gombe ya shiga hannu ’yan bijilante sakamakon sawa da ya yi a ka dauki hoton bidiyonsa ya na barazanar kisa ga Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari da Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe.

An nuno shi a bidiyon ya na cewa, idan sun kai su 1,000 irinsu za su haɗu su yi gunduwa-gunduwa da Shugban ƙasa Muhammad Buhari da Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe.

Usman Muhammad ya ce, ya furta hakan ne, saboda ya na fama da baƙin talauci, kuma ya na son gwamnati ta kula da shi, don ya samu yadda zai yi da rayuwa. Ya ce, ya na fama da Talauci ne sosai, domin a da ya na da shanu guda 70 da ya gada a gidansu kuma a ka qwace ma sa su a yankin Taraba, a ka kuma kashe ma sa makiyayin, sannan a ka kashe ma sa babban ɗansa mai shekaru 12.

Ya kuma ce, a baya ne lokacin da ya je kasuwar Iware a Jihar Taraba yayin dawowar da zai yi sai ya tarar da wannan aika-aikar da a ka yi ma sa ta kisan, a ka kuma kwashe shanun a ka yi gaba da su. Shi ne sanadiyar shigarsa wannan hali na quncin rayuwa da ta sa shi fitowa ya furta wannan kalami.

Usman ya ce, saboda bai da aikin komai a can Jihar Taraba, sai ya dawo Gombe ya nemi aikin gadi a unguwar GRA a na biyan sa albashi
na Naira 20,000, amma a cewarsa kuɗin sun yi ma sa kaɗan, saboda ya na da ‘ya’ya uku da matarsa ɗaya.

Ya ce, shi ne ya sa a ka ɗauke shi a hoton bidiyon, ya kuma bada izinin a tura a shafin sada zumunta na Facebook, don waɗanda ya yi barazar su gani, don su neme shi.

“Ban yi wannan furucin da gaske ba; na yi ne da niyyar gwamnati ta kalle, ni ko zan samu tallafi a rayuwa, ganin ya aikata wannan laifi da ’yan bijilante su ka kama shi za su miƙa shi ga hukuma, ya ce, ya na neman a yi ma sa afuwa; ba zai sake ba,
domin kuskure ne.

Da ya ke bayyana yadda su ka kama shi, Kwamandan ’Yan Biilante na Jihar Gombe, Abdullahi Ibrahim Dan Asabe, cewa ya yi, ya na zaune a ka kira shi a ka gaya ma sa cewa, ga wani bidiyo da aka tura a Facebook ya na yawo a na barazar kisa ga Gwamna Inuwa da Shugaban kasa su nemo shi. Shi ne ya baza yaransa cikin farin kaya, ya ba su awa 24 su nemo shi da ikon Allah kuma cikin awa shida su ka samu wanda ya san shi, su ka kama shi a wajen da ya ke aikin gadi.

Abdullahi Dan Asabe ya ce, wannan idan a ka bar shi irinsa ne su ke zama masu garkuwa da mutane, don karɓar kuɗin fansa ko ’yan ta’adda.Ya ce, a lokacin da su ka kama shi ya musanta cewa, ba shi ba ne ya furta wannan kalaman, amma sanda su ka kunna ma sa waya ya gani, sannan ya yarda ya amsa laifinsa.

Kwamandan ya ce, yanzu za su miqa shi ga DPO na gwaryar Gombe, shi kuma DPO zai miƙa shi zuwa ga Kwamishinan ’Yan Sanda, sannan su kuma su su ka san yadda za su yi da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *