Tsoho Dan Shekaru 80 Ya Yiwa Wata Marainiyya ‘Yar Shekara 10 Fyade A Yobe

Rundunar ‘yan sanda reshen jahar Yobe ta ce ta cafke wani tsoho dan shekaru 80, Mohammed Bara’u dake gundumar Lawan Fannami a Gashua, jahar Yobe, a kan zargin yiwa wata yarinya marainiyya ‘yar shekaru 10 fyade bayan ya ja ta zuwa dakinsa.

An kama tsohon ne bayan ‘yan kwamiin Shari’ar karamar hukumar tare da wasu ‘yan gundumar sun mika karar zuwa ga ‘yan sanda

An samu rahoton cewa tsohon mai sayar da itace ya ja ra’ayin yarinar ta hanyar saya ma ta alewa amma a ranar Lahadi da ya gabata tsohon ya samu nasaran aika yarinyar zuwa dakinsa dauko ma shi abu. Inda a nan ta ke bayan ta shiga dakin nasa shi ma ya bita sai ya ma ta fyade da karfi da yaji

Rahotonni na asibiti sun bayyana cewa an lalata budurcin yarin a yayin da shi tsohon ya furta aikata laifin da ake zarginsa da shi.

“Na yi lalata da yarin sau daya ne kawai” inji tsohon da yayi lalata da karamar yarinyar a yayin da yake hannun ‘yan sanda.

Ita yarinyar da aka yiwa fyaden ta kasance marainiyya ce ba ta da uwa balle uba.

Shi wanda ake zargi, Mohammed Bara’u za a aika shi zuwa ofishin CID da ke Damaturu a ranar Juma’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *