Shugabancin APC: An Maye Gurbin Oshiomole Da Ajimobi

Uwar jam’iyyar All Progressives Congress APC ta nada tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Ajibola Ajimobi, matsayin mukaddashin shugaban jam’iyyar.

Hakan ya biyo bayan hukuncin kotun daukaka kara da ta tabbatar da dakatar da Adams Oshiomole matsayin shugaban jam’iyyar.

Kakakin jam’yyar ta APC, Lanre Issa-Onilu ya bayyana hakan a shafin jam’iyyar na Tuwita da daren Talata, 16 ga watan Yuni, 2020.

Shugaban kungiyar gwamnonin APC Yace: “Kwamitin gudanarwan jam’iyyar All Progressives Congress APC ta samu labarin da ke nuna cewa kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin dakatar da shugaban uwar jam’iyya, Kwamred Adams Oshiomole, da wata babbar kotun Abuja tayi.”

“Bisa da ofishin lamuran dokanmu da kuma sashe 14,2 (iii) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar, mataimakin shugaban jam’iyyar (Kudu), Sanata Abiola Ajimobi zai zama mukaddashin shugaban jam’iyya.”

Mun kawo muku rahoton cewa Kotun daukaka kara da ke Abuja ta jaddada dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Talata, 16 ga Yuni, 2020.

Zaku tuna cewa a ranar 4 ga watan Maris ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar wasu mambobin APC shida na jihar Edo wajen dakatar da Oshiomhole.

Alkalan da suka samu jagorancin shugaban alkalan kotun daukaka kara, Mai shari’a Monica Dongban-Mensem sun yanke hukuncin cewa daukaka karar Oshiomhole bata da tushe.

Hukuncin ya zo ne a ranar da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya fita daga jam’iyyar APC bayan ganawarsa da Farfesa Ibrahim Gambari, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Hakazalika, Darakta janar na kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC, Salihu Lukman, ya bayyana cewa shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomole, ya sayar da rayuwar jam’iyyar ga wasu wadanda ke kokarin ganin bayanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *