Kano Za Ta Taimakawa Jam’iyyar APC Wajen Lashe Zaben Gwamna A Edo – Ganduje

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce jam’iyyarsa ta APC ta yi daidai wajen hana takwaransa na Jihar Edo, Gwamna Godwin Obaseki izinin sake takara a zabe mai zuwa.

Ganduje ya ce Jam’iyyar tabi matakan da suka dace wajen daukar matakin kuma su yanzu abin da ke gaban su shi ne samun nasarar zaben da sabon dan takarar da jam’iyyar za ta tsayar kamar yadda gidan Rediyon Faransa ya labarto.

Gwamnan ya ce Jihar Kano za ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin Jam’iyyar APC ta lashe kujerar gwamnan jihar Edo saboda yadda aka bi matakan da suka dace daki-daki.

A nashin bangaren, Gwamnan Jihar Ribas Nyesome Wike ya caccaki shugabannin jam’iyyar APC kan matakin da suka dauka na haramtawa Godwin Obaseki takara, inda ya ce zai yi iya bakin kokarinsa wajen ganin Gwamnan ya lashe zabe mai zuwa.

Rahotanni sun ce Jam’iyyar PDP na zawarcin Obaseki amma Gwamnan ya ce ba zai yanke hukunci kan makomarsa ba har sai ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *