‘Yan Bindiga Sun Kashe Mai Gari A Jihar Filato

A yammacin ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki a kauyen Kambang-Malul dake gundumar Daffo a karamar hukumar Bakkos, tare da kashe mai gari da kuma wani mutum daya.

‘Yan bindigar sun kashe mai garin malam Musa Ataka da Danjuma Taake a yayin da suka dawo daga ziyara

Wata majiya ta bayyana mana cewa,  wasu mutane ne suka tsinci gawar mai garin nan take suka  sanar sa iyalansu domin kai su dakin ajiye gawawwaki na asibitin  Luna.

Da aka tuntunbi kakakin hukumar ‘yan Sanda jihar dake hidikwatar ‘yan Sanda dake Mangu Mista Yusuf Balami,  ya tabbatar da faruwar lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *