Lokaci Ya Yi Da ‘Yan Kanywood Za Su Sanar Da Buhari Abin Da Ya Ke Faruwa – Rahama Hassan

Tsohuwar jaruma a masa’antar Kanywood Rahama Hassan, wacce tauraron ta ya haska matuka ta yi kira ga ƴan Kanywood da su tashi tsaye wajen yin kira ga shugaba Muhammadu Buhari akan matsalar tsaro da ta addabi yankin arewacin ƙasar nan, kamar yadda su ka cika kafafen sadarwa na zamani da neman a zaɓe shi a lokacin da ya ke neman zaɓe a karo na biyu.

Rahama Hassan ta bayyana hakan ne a shafinta na fasebuk, inda ta buƙaci mashahuran mutane da ƴan Kanywood din su gayawa shugaba Buhari gaskiyar abin da ya ke faruwa a ƙasar nan.

“Gareku ƴan Kanywood da duk wasu mashahuran mutanen da su ka taya jam’iyyar APC tallata shugaban ƙasa na neman takara zango na biyu ƙarkashin Taken NEXT LEVEL”

Ta ƙara da cewa kun yi amfani da soyayar da talakawan wannan ƙasa su ke muku kuka sa ka su suka sake zaben Buhari, kuma sun amsa sun zabe shi, to in har da gaske kun yi haka ne domin son ganin an yi gyara a wanann kasa ne to yana da kyau ku fito ku sanar da shugaban ƙasa halin da talaka ya ke ciki na rashin tsaro da yake fama dashi a wannan kasar.

“Ku tashi tsaye wajen yin kira ta shafukanku da ku ka taya shi yakin neman zabensa. Domin wallahi akwai ƙauyuka da yawa da basu iya bacci mai kyau da daddare saboda fargaba da tsoro da yake addabarsu.
Idan ba ku yi haka ba wallahi ku tabbata kunci amanar talakawan Najeriya da Masoyan ku”

Idan za a iya tunawa dai tsohuwar jarumar ta auri mijinta Alhaji Usman Sani El-kudan a ranar 6 ga watan janairu na shekara 2017 a mahaifar ta da ke garin Suleja nan jihar Niger.

Rahama Hassan ta fito a fina-finai da dama masu kayatarwa cikin su akwai ”Birnin Masoya’, ‘Dan Marayan Zaki’ da ‘Karangiya’.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *