Jam’iyyar APC Ta Kasa Ta Yi Gaskiya A Kan Siyasar Edo – Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya goyi bayan Shelkwatar APC ta kasa akan irin wainar siyasar da ake toyawa a jihar Edo yana mai cewa Jam’iyyar tafi damuwa da abin da doka tace a maimakon duk wani uzuri.

Ya bayyana ra’ayin nasa ne ranar litinin a dakin taro da ake kira Africa House dake fadar Gwamnatin jihar Kano lokacin tattaunawa da ‘yan jarida dake aiki a jihar.

“Jam’iyyar mu ta APC tafi damuwa da abin da doka ta tanadar akan wannan lamari a maimakon duk wani uzurin da za a kawo.

Shin kun tuna zaben Gwamnan Jihar Bayelsa?

Mun ci zaben amma maganar bin abin da doka tace ta sa aka bar maganar cin zaben da mukayi”, inji Gwamna Ganduje.

Ya kara da cewa “ina mai tabbatar muku, Shelkwatar APC ta kasa tana iyaka kokarin ta wajen ganin APC ta lashe zaben”, Muna da duk wasu dabarun da suka dace”.

Gwamnan yace “irin wannan hayaniya da cece kuce abu ne da dama can an saba da shi a siyasa yana mai cewa kada kowa ya tada hankalin sa ko yayi tsammanin hakan zai haifar da wata matsala.

A ƙarshe Gwamnan ya ce Babu wata matsala, zamu bi duk wata hanyar da ta dace bisa doka domin samun nasara”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *