Harbi A Fadar Shugaban Kasa: Buhari Ya Bada Umarnin Bincike

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayar da umurnin a yi bincike a kan matsalar tsaro da aka samu a ranar Alhamis wanda har ta kai ga yin harbi da bindiga a farfajiyar fadar ta shugaban kasa.

Cikin wata sanarwa a jiya, fadar ta shugaban kasa ta yi nuni da cewa sam lamarin ba cikin fadar ne ya auku ba, hakan bai kuma nuna wani hadari ga lafiyar shugaban kasan ba.

Sanarwar wacce mai taimaka wa shugaban kasan na musamman a kan harkokin manema labarai da wayar da kai, Malam Garba Shehu ya fitar, ta kuma ce shugaban kasa Buhari zai bari doka ta yi aikinta a kan aukuwar lamarin.

Sanarwar ta nuna rashin jin dadinta a kan yanda ‘yan hamayya suke yayata lamarin, musamman a kan yanda suke bayar da misalin ta wajen soke-soken su ga shugaban kasa.

Shehu ya ce: “Fadar shugaban kasa tana son nuna rashin jin dadinta a bisa damuwar da mutane da yawa suke nunawa a kana bin da ya auku a tsakanin mazauna fadar ta shugaban kasa wanda har ya kai ga kama wasu ma’aikatan fadar da ‘yan sanda suka yi.

“Wannan sanarwar tana son sanar da al’umma ne cewa, ko kusa shugaban kasa kuma babban kwamandan rundunonin mayakan kasar nan ba ya fuskantar wani hadari, ko dai daga annoba ko kuma na abin da ya auku a tsakanin jami’an tsaro wanda a halin yanzun ake kan binciken sa.

“Wannan abin da ya auku din ma ya auku ne a wajen ainihin ginin gidan na shugaban kasa. Dukkanin masu tsaro da sauran hukumomin tsaro da suke aiki a fadar ta shugaban kasa suna da cikakkiyar kwarewa, musamman ta yanda ya kamata su yi aiki da makamai da kuma sauran matsalolin da suka yi kama da hakan.

“A bayan bayar da umurnin yin cikakken bincike a kan wannan abin takaicin da ya auku na ‘yan sanda, shugaban kasa ya bayar da umurnin barin doka ta yi aikinta.

“Dan wannan abin da ya auku din wasu masu suka suna yin amfani da shi wajen bayyana soke-soken su ga gwamnati da kuma shi kanshi shugaban kasa Muhammadu Buhari.

“A kan wannan abin da ya auku din shugaban kasa yana mai cewa lallai a bar doka ta yi aikinta,” in ji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *