Gwamnatin Kano Za Ta Rage Kasafin Kuɗin 2020 Da Kaso 30%

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da cewa kwanan nan gwamnatin jihar za ta rage kasafin kuɗin jihar na 2020 da kaso 30% don ta samu ta kammala ayyukan da ta riga ta fara, kamar yadda jaridar Intanet, ‘Daily Nigerian ta rawaito’.

Gwamnan, wanda ya bayyana haka a yayin wata tattaunawa da manema labarai a Kano ranar Litinin, ya ce ɗaukar wannan mataki ya zama wajibi biyo bayan samun raguwa a Kuɗaɗen Shiga na Cikin Gida, IGR.

A cewar Gwamnan, samun ragin da aka yi ya tilasta gwamnati ta kula sosai wajen kashe kuɗaɗe don ta samu ta iya kammala ayyuka kafin ƙarshen wa’adin mulkinsa.

“Annobar COVID-19 ta kawo matsalolin kuɗi da dama. Muna fata za mu kammala ayyukanmu kafin ƙarshen wa’adin mulkinmu. Raguwar IGR ya sa dole mu kula sosai da yadda muke kashe kuɗi.

“Dole mu yi kaffa-kaffa game da yadda muke kashe kuɗi saboda muna son kammala ayyukanmu, shi yasa nan ba da daɗewa ba za mu kai wa Majalisar Dokoki ta Jiha kasafin kuɗinmu don ta yi bitar sa.

“Za mu yi aiki don rage kasafin kuɗin da kaso 30% saboda muna son cimma burinmu na kammala ayyuka”, in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *