MC Tagwaye Ya Angwance Da Ɗiyar Hadimar Buhari

Mai wasan barkwanci, Obinna Simon, wanda aka fi sani da ‘MC Tagwaye’, ya angwance da amaryarsa Hauwa, diyar Maryam Uwais, mai baiwa shugaban kasa shawara a kan harkokin jin dadin ‘yan kasa.

Da safiyar ranar Lahadi ne Maryam Uwais, uwar amarya, da kanta ta yada hotunan bikin MC Tagwaye da Hauwa a shafinta na dandalin sada zumunta.

“A yau ne diyata, Hauwa, ta yi aure. Na yi sabon ɗa, MC Tagwaye. Za su kasance cikin soyayya, raha da barkwanci duk inda suka samu kansu, daga nan har zuwa karshen rayuwarsu.

“Ina neman ku taya wadannan sabbin ma’aurata murna da addu’a. Aure ba abu ne mai sauki ba. Amma addu’arku da taimakon Ubangiji zai taimakesu a cikin rayuwarsu ta aure,”.

Da yake magana a shafinsa na dandalin sada zumunta ranar Asabar, ango MC Tagwaye ya rubuta: “wannan rana ta kasance mai muhimmanci, mun dora daga wurin da muka tsaya.

Ga masu tambaya, lallai an daura mana aure a yau.”

MC Tagwaye ya fara shiga bakin ‘yan Najeriya bayan ya kwaikwayi murya da salon zancen shugaba Buhari domin gabatarwa da ‘yan Najeriya jawabi amadadin shugaban kasa.

Mai wasan barkwancin, dan asalin jihar Anambra, ya ce ya kasance malamin makaranta da ke samun ‘yan karin ‘yan kudade daga wasan barkwanci bayan albashinsa..

“Na kasance malamin makaranta na tsawon shekaru fiye da bakwai. Ina koyarwa, ina gwada wasan barkwanci domin tallafawa albashin da nake samu.

“Ina kokari sosai wajen ganin cewa na kwaikwayi kowanne mutum ba tare da samun banbanci mai yawa ba. “Yanayi da salon maganar Buhari sun fi zama a jikina sosai har ma na kasa komawa yadda nake tun asali.

“Hatta shugaba Buhari takatsantsan yake yi wajen magana lokacin da na ziyarce shi, saboda ba ya son ya fadi wani abu da zan kara rikewa na cigaba da kwaikwayonsa.

“Duk masu kaunar Buhari suna kaunata, haka makiyansa ma sun tsaneni,” kamar yadda MC Tagwaye ya shaidawa BBC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *