Auren Wasa Dai Ya Tabbata Gaskiya Tsakanin Wasu Masoya Biyu A Jihar Neja

Da misalin ƙarfe biyu na ranar yau 13 ga waran Yunin 2020 ne aka ɗaura auren Jamilu da Nasiba waɗanda suka fara zancen auran nasu a ranar litinin 9 ga watan yunin 2020 kamar da wasa a garin Kontagora ta Jihar Neja, labarin da jaridar Rariya da Niger State Media News24 da sauran kafafen sadarwa suka wallafa tare da gabatar da shirye shirye a gidajen radio daban daban akan auran wanda yaja hankalin duniya inda al’umma dadama suka ta bayyana ra’ayoyin su mabanbanta dangane da al’amarin.

An ɗaura auren ne a garin Libele dake ƙaramar hukumar Magama a Jihar Neja biyo bayan sadakin naira dubu ashirin lakadan da ango ya biya, inda aka gabatar da sigar aure kamar yadda addinin musulunci ya tanadar malammai kuma sukayi addu’o’i da fatan alheri akan auran.

Ɗaurin auran ya samu halartar ɗinbin al’umma daga kusurwa daban daban waɗanda suka halarci garin domin shaida ɗaurin auran dake cike da abun mamaki da farin ciki. Jimkaɗan bayan kammala ɗaurin auren wakilin mu ya samu zantawa da angon mai suna Jamilu Yusuf inda ya bayyana matuƙar farin cikin sa tare da godiya ga ƴan uwa da abokan arziki da ɗaukacin al’umma na irin gudunmuwa da addu’o’in fatan alheri da suka riƙayi mai dangane da auran nasa.

Daga: Comrade-Zakari Y Adamu Kontagora

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *