Rashin Tsaro: Matasa Sun Sake Gudanar Da Zanga-zanga A Katsina

A ranar Alhamis ne daruruwan al’ummar kauyen Yankara dake karamar hukumar faskari suka fito kan titi cikin fushi tare nuna bacin ransu game da gwamnatin tarayya take nuna halin ko in kula ga rayuwarsu, sakamakon aikin ‘yan ta’adda a yankin nasu wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 60 a ‘yan kwanakin nan.

Matafiya daga garin Kaduna, Zaria da Futuntua masu zuwa Zamfara da Sokoto basu damar wucewa sakamakon rufe titi da masu yin zanga-zangar yi. Haka nan wanda wanda suka taso daga Kano zasu bi ta hanyar Sheme su ma basu samu hanyar wucewa ba.

Daga cikin wanda suka gabatar da zanga-zangar akwai matasa da dama wanda suke dauke da allon-rubutu mai dauke da rubutu kala-kala inda suke tuhumar gwamnatin tarayya game da rashin tsaro da suke fuskanta a yankin nasu.

Abubakar Hamisu daya daga cikin masu zanga-zangar ya shaidawa wakilinmu cewa, wannan rashin imani yayi yawa gwamnati kuma bai dameta ba saboda ba iyalansu ake kashewa ba.

Wata mata daga cikin matafiyan, wadda ta taso daga Kano zuwa garin Gusau, ta bayyana jin dadinta na yadda masu zanga-zangar ke bayyana damuwarsu cikin lumana ba tare da bata kayan gwamnati ba.

Ta ce “bai kamata ana kashe rayukan al’umma ba, kuma a ce gwamnati tayi shiru bata yi komai akai ba”.

Wannan zanga-zangar dai ya biyo bayan wadda aka gudanar kwanaki biyu da suka wuce a kauyen Yantumaki dake kamarar hukumar Danmusa.

Sai dai a jiyan, majiyarmu ta sanar da mu cewa, gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya shiga ganawar sirri da masu ruwa da tsaki na jihar kan matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar ta Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *