An Cafke Magidancin Da Ya Yiwa Mata 80 Fyade A Kano

Wani magidanci da yake bi gida-gida yana yi wa mata fyaɗe a ƙauyen Kwanar Ɗangora dake jihar Kano ya zo hannu, bayan da mutane suka yi tara-tara suka cafke shi, kuma suka yi masa tumɓur.

Wani rahoton shirin In Da Ranka na Freedom Radio da Labarai24 ta bibiya ya bayyana cewa a cikin matan da mutumin mai suna Maisiket ya yi wa fyaɗe har da wata tsohuwar ‘yar shekara 80.

“Na fita zan tafi aikin ne sai aka kama ni. Na shiga wani gida kenan a lokacin”, in ji shi.
Da aka tambaye shi ya yi wa mata kamar nawa fyaɗe?

Sai ya ce: “E za su kai 40”.

E. A nan Kwanar Ɗangora. Akwai wata dattijuwa ma da na je na samu, a nan Kwanar Ɗangora, ban san sunan unguwar ba gaskiya”, in ji Maisiket.

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano, ta bakin Mai Magana da Yawunta, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, tabbatar da kama Maisiket, ya kuma ce za su gurfar da shi a gaban kotu.

“Daga tambayoyi da muka yi masa na farko, ya tabbatar mana da cewa faɗe aikinsa ne, wanda a cikin shekara ɗaya ya yi wa mata sama da 40 kama daga ƙananan yara, manyan mata da kuma tsofi, wanda yanzu haka mun fara samun masu zuwa su shigar da ƙorafi, har da tsohuwa ‘yar shekaru 80 da ya yi mata faɗe.

“Da zarar mun kammala bincike za mu gurfanar da shi a gaban kotu domin ya girbi abubuwan da ya shuka”, in ji Mista Kiyawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *