Meye Shugaban Kasar Chadi Idris Derby Yafi Shugaba Kasar Najeriya Buhari? – Daga Kabiru Ado Muh’d

Shugaban kasar chadi idriss deby ba Soja bane don be tabayin aikin Soja ba.

Amma a lokacin da yan ta addan kasar tasa suka addabi wasu yankuna Na kasar tasa da kashe kashen al ummar dayake mulka, ya fita yabar Gidan gwamnatin kasar da kansa ya jagoranci rundunar sojojin kasar suka yankunan da yan ta addan kasar suke cin karensu ba babbaka ya tare.

Idriss deby be baro dokar jejin nan ba seda ya tabbatar ya karya lagon yan ta addan da suka addabi al ummar dayake mulka.

Shugaba Buhari tsohon sojan yaki ne tunkafin yayi gwamna a borno kuma yayi shugaban kasa Na mulkin Soja ya ziyarci yakukkuna da dama.

Me zai hana shugaba Buhari yayi kamar yadda shugaban kasar chadi idriss deby yayi, shima ya tattara yanasa yanasa yadawo jihar Katsina mahaifarsa da zama, yayi binciken ta addan cin dake addabar yan uwansa tare da bincikar ainahin wadanda suke daukar nauyinsu dakansa a matsayin Sa Na tsohon sojan yaki daya kware a harkar tsaro..

Sannan ya umarci mataimakinsa yemi osinbajo daya koma garin borno duk suci gaba da aiwatar da irin aikin da shugaban kasar chadi idriss deby yayi a kasar Sa.

Idriss deby fa ba Soja bane be tabayin aikin Soja ba amma yayi haka, meyasa shugaba Buhari bazaiyi haka ba shida yake tsohon sojan yaki ma.?

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *