Gobara Yayi Sanadiyyar Mutuwar Wata Mata Da Yaranta 3 A Neja

A ranar Talata ne wani tsautsayin wutar gobara yayi sanadin rasuwar wata mata tare da yaranta su uku ciki har da jariri dan wata daya a duniya, inda suka kone kurmus a anguwar Nkangbe dake Minna, babban birnin jihar Niger.

Sai dai daya matar gidan an yi nasarar ceto rayuwarta da ta ‘ya’yanta, kuma an dauke su zuwa asibiti sakamakon mummanr kuna da suka samu.

Gobarar dai babu wanda zai bayyana abinda ya haddasa ta, amma ta dauki tsawon sa’o’i biyar tana ci kafin a kashe ta daga bisani.

Hukumar kashe gobara tayi kokarin kashe wutar bayan da ta samun kiran agaji, sai dai basu damar ceto matar da yaranta ba sakamakon karfen kariya (burglary) da aka sa a tagar dakin wanda ta hana su samun hanyar shiga domin ceto mamatan.

Wani wanda ya ganewa idonsa faruwar gobarar Ahmed, ya bayyana cewa yankin sun dauki tsawon watanni biyu basu da wutar lantarki a yankin sakamakon lalacewar na’urar wuta lantarki.

“Mutanen gidan suna ciki a lokacin da muka ga hayaki ya fara fitowa daga gidan, sai muka kira jami’an kashe gobara kuma nan take suka zo, mun yi kokarin kashe wutar amma bamu iya ba saboda wutar da karfinta take ci”.

“Da taimakon jami’an kashe gobara mun samu nasarar ceto daya matar tare da yaranta, sai dai sun samu mummanr kuna a jikinsu”.

Jami’in hukumar kashe gobarar, ya bayyanawa wakilinmu cewa har yanzu ba a san abinda ya haddasa gobarar ba.

“Lokacin da muka zo mun kasa ceton matar ita da yaranta saboda yanayin irin tsarin ginin da aka yiwa dakinta, amma daya matar an samu ceto da kuna mai yawan gaske a tare da su”.

Ya kara da cewa “yanzu dai muna adadin mutane hudu da suka rasu, sai kuma mutane uku da suka kone, mun kasa ceton daya matar ne saboda karfen kariya na rodi da aka a jikin tagar dakin wanda ya ki fita har rai yayi halinsa” Cewar jami’in.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *