Badakallar Filin Biliyan N2.2: Sanusi Ya Daukaka Kara

Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya ɗaukaka ƙara game da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya dake Kano ta yanke, wadda ta yi watsi da buƙatarsa ta a saurare shi game da binciken da Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano, PCACC, ke yi masa.

Majiyarmu ta rawaito cewa lauyoyin tsohon Sarkin ne, Dikko da Mahmud suka ɗaukaka ƙarar ranar Laraba.

Tsohon Sarkin ya roƙi kotun ta ba shi kariya game da binciken da PCACC ke yi masa kan zargin wata badaƙalar fili ta biliyan N2.2.

Sai dai Mai Shari’a Lewis Alagoa ya yi watsi da buƙatar tsohon Sarkin, ya kuma ba hukumar damar ci gaba da binciken zargin badaƙalar filin.

“Ƙari bisa sanarwar ɗaukaka ƙara, mun kuma shigar da ƙarar dakatar da bincike har sai an saurari ɗaukaka ƙarar wanda muke karewa.

“Muna da yaƙinin cewa ɗaukaka ƙarar yana bisa ka’ida da hujjoji, kuma dokar da take gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara za ta ba wanda muke ba kariya nasara. Kuma wanda muke ba kariya zai ci gaba da bin shari’ar har zuwa ƙarshe.

“Bisa waɗannan abubuwa da suka gabata, an dakatar da dukkan wasu matakai game da wannan batu ba tare da ɓata lokaci ba, kuma masu ƙara su ƙaurace wa duk wani abu da ka iya zama riga Malam masallaci ga Kotun Ɗaukaka Ƙara”, in ji Mista Dikko da Mista Mahmoud.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *