Rashin Isashen Jima’i Kan Iya Sanyawa Cutar Tabin Hankali – Masana

Wata likita wacce ta shahara a bangaren kwakwalwan dan Adama wato psychiatrist, Dr Maymunah Kadiri, ta shawarci mata da su rinka saduwa da mazajensu a kai a kai domin ya rage masu damuwa da kuncin da ke damunsu tare da sa su jin dadi

Kadiri, wacce ta kasance likita ce a asibitin Pinnacle Medical Services ta shawarci mata da su rinka kusantar mazajensu a wani hira da aka yi da ita inda ta ce jima’i ba wai kawai yana gyara jikin ‘ya mace bane har da yadda kwakwalwanta ke aiki yana gyarawa.

“A matsayin mu mata ya kamata mu mayar da mazajen zaman mu tambar abokan mu idan har muna so mu samu lafiya da kwanciyar hankalina. Bincike ya nuna cewa mata masu yawan jima’i a kai a kai basu cika samu hawan jini ba kamar wadanda basu samu jima’i a kai a kai.

Saboda haka, jima’i yana da matuka fa’ida. Yana daya daga cikin abubuwan da ke rage yawan samun ciwon kai ga ‘ya mace. Rashin samun isashen jima’ai yana janyo damuwa sosai.

Mata su kan shiga cikin damuwa idan har basu samun isashen jima’i a kai a kai kamar yadda suka saba. Yawaita yin jima’i yana taimakawa mata sosai matuka musamman ga lafiya su” inji Kadiri.

Ta kara da cewa ba wai kawai an yi jima’i bane domin a haihu bane kawai ko kuma a samu yara bane kawai. Jima’i yana kara dankwon soyayya a tsakanin ma’aurata tare da kuma sanya bacci mai dadi.

Kadiri wacce aka fi sani a matsayin likitan jarumai na Nollywood ta yi kira ga mata masu fama da damuwa da su yawaita jima’i da mazajensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *