Mahaukaci Ya Ja Matafiya Sallah A Damaturu

Wasu matafiya a unguwar Bayan Tasha dake Damaturu, babban birnin jihar Yobe, sun bi wani mai taɓin hankali salla bisa rashin sani.

A cewar wani rahoton shirin In Da Ranka na Freedom Radio, Kano da Labarai24 ta bibiya, matafiyan sun zo ne a matsayinsu na baƙi, sai suka tarar limamin yana gabatar da sallar Azahar, hakan ne yasa suka fara bin sa.

A cewar rahoton, bayan limamin ya yi raka’a huɗu, sai ya ƙi zama, sai ya miƙe ya kawo ta biyar, suna ta yi masa tasbihi amma bai kula su ba.

A haka dai suka ci gaba da bin sa har sai da ya yi raka’a shida, bayan da suka fuskanci akwai matsala ne sai suka yi sallama.

Jim kaɗan bayan sun sallame, sai limamin ya ci gaba da sallarsa.

Hakan ya jawo hankulan mutanen dake wajen, inda suka ankarar da masallatan cewa limamin da suka bi fa mahaukaci ne.

“Mun yi alaula mun taho masallaci na kan hanya, kawai sai muka ga mutum da kaya mai kyau haka, kamar mai hankali sai muka jona masa salla.

“Da muka jona masa salla, sai aka yi raka’a biyu, da aka yi raka’a biyu mai kyau aka yi tahiya sai aka tashi. Da aka tashi sai aka yi raka’a biyu, maimakon a zauna sai aka yi ta uku, muka ce subhanalLah sai ya ƙi kula mu. Aka sake raka’a ɗaya, sai wani yana wucewa sai ya ce ai mahaukaci kuke bi salla. Kawai sai muka watse muka bar wannan wurin”, in ji ɗaya daga cikin waɗanda suka bi mai taɓin hankalin salla.

Freedom Radio ta tuntuɓi wani malami a Kano, Dakta Ahmad Abdullahi Ibrahim Daneji don jin matsayin bin mai taɓin hankali salla.

“Wanda ya bi mutum salla, daga baya ya gano cewa wannan mutumin mahaukaci ne, bayan an idar da salla, malamai sun haɗu cewa ya zama wajibi a gare shi ya rama sallarsa, kamar yadda Imamun Nawawi ya faɗa.

“Wannan shi ne abinda malamai suka haɗu a kai””, in ji malamin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *