Boko Haram: Mayakan Sun Kai Awanni 6 Suna Yi Mana Wa’azi Kafin Suka Kashe Muatne 81 – Matashin Da Ya Sha Fadawa Zulum

Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Laraba, ya ziyarci kauyen Faduma Kolomdi da karkashin karamar hukumar Gubio, inda ya mayakan Boko Haram suka kai hare, suka kashe yara, maza da mata.

Kauyen Faduma Kolomdi ya kasance kauyen makiyaya ne, sannanan yana nisan kilomita 35 daga arewacin Gubio, hedikwatar karamar hukumar Gubio a jahar Borno.

Wani matashi wanda ya samu tsira daga haren da mayakan suka kai ya fadawa gwamna Zulum cewa mayakan sun kashe mazauna kauyen 81 a yayin da suka kai harin a ranar Talata sanna kuma wasu mutane 13 sun jikkata sannan mayakan sun sace wasu mutane 7 a ciki hadda mai garin.

A yayin ya ke yiwa alumma jimami gwamna Zulum yayi kira ga sojojin Najerya da su hanzarta wajen kawo karshen wanna kashe kashen da mayakan ke yi a ta bangaren mahadar Najeriya da Chadi

Zulum yayi Allah wadai da haren da mayakan suka kaiwa kauyen. Inda ya tafi da mutane zuwa asibiti domin su samu kulawa na musamman.

“A shekaran da ya gabata, mayakan sun kashe kusan mutane kamar haka a kauyen Gajiram. Allah wadai da hakan. Yadda za kawo karshen wannan ta’addanci shine kawai a nakasa mayakan da ke zama a mahadar bodar Najeriya da Chadi. Yin hakan na bukatar hadin kan mazauna yankin,: inji Zulum

Wani matashi wanda shi kadai ya samu nasaran tsira daga haren da mayakan suka kai ya bayyanawa gwamna Zulum abunda ya faru a yayin da ya ziyarci kauyen.

Ya bayyana labarinsa kamar haka, “Mayakan sun shigo kauyen ne a cikin motocin masu dauke da bindigogi da misalin karfe 10{00 na safiyar jiya (Talata). Sun tara duk alumma kauyen a wuri daya sannan suka yi mana wa’azi. Sai suka bukace mu mu mika duk wani makamai da muke da su a kaueyn. Wasu mazauna kauyen suka mika makaman nasu.

“Mayakan suka nuna mana kamar ba za su yi mana komai ba. Kawai sai suka fara harben mu. Hadda kananan yara da mata ba su bari ba, mafi yawanci a harbe su a kusa hakan ya sa basu tsira ba. A nan ne wasu suka fara gudu. A karshe dai, an kashe mutane da dama.

“Mu ta binne mutane dtun karfe 10:00 na dare har zuwa 6:00 na safe. Mun binne gawarwaki 49 a yayin da za mu kai wasu 32 zuwa ga iyalansu da ke kusa da kauyen mu. Mayakan sun sace mutane 7 a ciki hadda mai gari. Sannan suka tafi da shanu 400,” ya ce.

=

An gano cewa mayakan ba su bankawa kauyen wuta ba kamar yadda suka saba yi idan sun kaiwa kauye hari. Wani mai zama kusa da kauyen da abun ya faru ya fadawa manema labarai abunda wani ya samu tsira daga hannun mayakan ya fadawa Zulum.

A halin yanzu mazauna kauyukan dake kusa da kauyen da mayakan Boko Haram suka kai hari suna a hirgice, domin suna ganin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin za su fi sama da 81

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *