Mahaifina Zai Yi Takarar Shugaban Ƙasa A 2023 – Ɗan Atiku

Adamu Atiku Abubakar, ɗan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya tabbatar da cewa mahaifinsa zai yi takarar Shugaban Ƙasa a 2023.

Atiku Abubakar shi ne ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen Shugaban Ƙasa na 2019, sai dai Shugaba Muhammadu Buhari ya kayar da shi.

A cewar Mista Adamu, wanda ya yi jawabi a wajen bayanin irin nasarorinsa a matsayinsa na Kwamishinan Ayyuka da Makamashi na jihar Adamawa, ya ce ba makawa mahaifinsa zai yi takara a 2023.

“A ra’ayina, ba na ganin wani kuskure idan mahaifina ya yi takarar Shugaban Ƙasa.

“A 2023, mahaifina zai yi takarar kujera mai daraja ta ɗaya a ƙasar nan saboda ya kasance gogagge, mai dabara, babban ɗan siyasa kusan tsawon shekara 40”, in ji shi.

Daily Trust ta tuntuɓi Paul Ibe, mai ba Atiku shawara kan kafafen watsa labarai, amma ya yi alƙawarin zai kira.

Mista Abubakar ya kasance Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya daga 1999 zuwa 2007 a lokacin shugabancin Olesegun Obasanjo.

Tun lokacin da aka dawo mukin dimokuraɗiyya, Mista Abubakar ya sha yin takara a dukkan zaɓukan Shugaban Ƙasa.

A sau biyu ya yi takarar Gwamnan jihar Adamawa, a 1990 da kuma a 1998 lokacin da aka zaɓe shi a matsayin Gwamnan Adamawa kafin ya zama abokin takarar Olesegun Obasanjo a lokacin zaɓen Shugaban Ƙasa na 1999 da na 2003.

Ya zama ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar AC a zaɓen Shugaban Ƙasa na 2007.

Ya shiga zaɓen fitar da gwani na PDP a zaɓen Shugaban Ƙasa na 2011.

A 2014, ya shiga jam’iyyar APC gabanin zaɓen Shugaban Ƙasa na 2015 ya kuma shiga zaɓen fitar da gwani, inda Shugaba Muhammadu Buhari ya kayar da shi.

A 2017, ya dawo PDP, kuma shi ya yi wa jam’iyyar takara a zaɓen Shugaban Ƙasa na 2019.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *