Hotuna Gudaji Kazaure Da Amaryarsa ‘Yar Kasar Senegal

Fitaccen ɗan majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Muhammad Gudaji Kazaure yayi sabuwar amarya, ƴar kasar Senegal.

Auren wanda aka ɗaura shi a ranar alhamis din da ta gabata, 4 ga watan Yuni, kamar shafin mujallar Tozali ya wallafa hotuna da katin gayyatar ɗaurin auren.

Tun da farko an daura auren ba mutane da yawa saboda ana tsaka da fama da cutar Coronavirus wacce ta jawo hana taruwar mutane da yawa a guri daya.

Muhammad Gudaji Kazaure wanda ya shahara wajen tsayawa ya yi magana a zauren majalisar gaba-gadi ba tare ko da yin ɗar na yin kuskuren harshen turanci da aka saba magana da shi a majalisar ba.

Ko a baya-bayan nan ɗan majalisar ya bayyana cewa zai nemi ganawa da shugaba Buhari don bayyana masa halin taɓarɓarewar tsaro da wasu yankunan ƙasar nan ke ciki.Honorabul Gudaji Kazaure ya ce yana da hujjoji da wasu ƙwararan shawarwari da zai bai wa shugaban kuma ya yi imani za su yi amfani wajen shawo kan matsalar tsaron da ake fama da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *