Ga Kadan Daga Cikin Illolin Da Ke Tattare Da Tsaka

1. Idan aka bar kowane irin garin abinci a bude, ta kan shiga tayi birgima a cikin garin. Bayan an tuka wannan garin, yawanci an kamu da cutan barasu wato kuturta ko wasu mugayen kuraje.

2. Idan aka bar ruwan sha a bude sai tayi amai a cikin ruwan bayan ta sha ruwan. Yawanci sai ka ga an kamu da shanyewan jiki wato paralyze ko kuma lallacewar sassan jiki.

3. Idan mutum ya kwanta bacci bai yi addu’a ba, ta kanye busa a cikin idon mutum. sai ka ga yawanci an samu lalacewar gani mai kyau ko a makanshe.4. Idan tsaka ta rika, misalin ire-iren gobara da ta ke faruwa a yanzu so da dama tsaka ce amma bamu sane ba, domin ita tsaka tana tare da mugayen jinnu. Dama Fiyayyen Halitta Ya ce, ita ce tayi busa ga wutan da aka jefa Annabi Ibrahim (A.S).

5. An ta samu labarin wata mata da ta tafasa ruwan shayi da tsaka a cikin butan shayin, a sanadiyar wannnan tsakar ita da mijin ta, da yaran suduk suka bakunci lahira.

Kadan kenan daga cikin ilolin tsaka saboda haka mu kula da ita wannan dabba wadda ta ke mu’amala a cikin gidajen mu, mi kula da abincin mu da abun shan mu, domin mu kauracewa wannnan illar da wannan dabba.

Idan mun gan ta a cikin gida, a yi kokarin kashe ta kuma a anbace sunan Allah (S.W.T) domin tana tare da shaidanu don tana cutar da mutane.

A yi amfani fa tsintsiya,

ko takalmi wajen kashe ta,

ko kuma a sa mata maganin kashe kwari

A dukkan lamarin mu, mu dun ga sa tsafta a ciki, tsafta gaskiya ne haka kuma Addini ma gaskiya ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *