Za’a Fito Da Wani Sabon Salo Agasar Firimiyar Ingila

Akwai yiwwuwar za a fito da wani sabon salo agasar ajin Firimiya ta kasar Ingila wanda babu irinsa koda a sauran gasar rukuni-rukuni ta sauran kasashe da ake gudanarwa a kasashen turai.

Sabon salon daza a fito dashi awannan gasa dai shine za a gayyaci masu daukan fefen bidiyo na talebijin a dakin sanya kaya wato dressing room.

An bayyana cewar za a dawo fafata gasar ajin Firimiya ta kasar Ingila aranar 17 ga watan Yuni inda za a fara da kwantayen wasanni guda biyu wanda yahadar da wasan Manchester City da Arsenal da kuma na Asoton Villa da Sheffield United.

Shin ko wannan sabon salo daza a fito dashi a gasar ta ajin Firimiyar Ingila zaikawo wani ci gaba? tambayar da jaridar Labarai24 tayiwa Abubakar Pepe dake jahar Kano kuma masani a harkar wasanni.“Eh ni aganina zai iya kawo ci gaba saboda yadda naga anakawo abubuwa dasuke karawa harkar wasanni kwalliya da wayar dakai yadda yakamata”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *