Yadda Ake Hada Yam Balls

Abubuwa Da Ake Bukata Wajen Hadi:


Doya 1
Nikakken nama
Kwai 4
Albasa 4
Attarugu 4
Mai
Maggi
Gishiri
Curry

Yadda ake yi :


A dafa doya sannan a bubbuga ta tayi laushi sai a hada ta da nikakken nama, a yanka albasa da attarugu, a zuba maggi, curry da gishiri. A motsa sosai sannan a rika curawa kamar kwallo, sai a tsoma a cikin ruwan kwai sannan a soya a mai

.
Idan ana bukata, ana iya saka kifi a maimakon nama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *