PDP Ta Roƙi Buhari Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa N70

Jam’iyyar hamayya ta PDP ta roƙi Gwamnatin Tarayya da ta rage farashin man fetur zuwa N70 duk lita.

A baya dai Gwamnatin Tarayya dai ta rage farashin man fetur daga N145 zuwa N125, sannan ta ƙara rage wa zuwa N121 a ranar Talatar nan, kamar yadda The Nation ta wallafa.Sai dai jam’iyyar PDP a cikin wata sanarwa da Sakatarenta na Yaɗa Labarai, Kola Ologbondiyan ya fitar ranar Talata ya ce Gwamnatin Tarayya tana cutar ‘yan Najeriya ne da farashin man fetur mai tsada.

Jam’iyyar ta ƙalubalanci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta rage farashin man fetur ɗin zuwa N70 duk lita don bada farashi mai kyau biyo bayan faɗuwar farashin man fetur a kasuwar duniya.

“PDP ta yi watsi da farashin N121 da Gwamnatin Tarayya ta sanar, farashin da an kasa ma tabbatar da shi”, in ji sanarwar.

Babbar jam’iyyar hamayyar ta bayyana sabon farashin man fetur da gwamnati ta sanar a matsayin abin harzuƙa jama’a da kuma rashin nuna damuwa da matsalar da ‘yan Najeriya suke ciki “musamman a lokacin da suke fama da matsalolin zamantakewa da na tattalin arziƙi da annobar COVID-19 ta haifar.
PDP ta jaddada cewa farashin N121 ya yi kama da cutar da ‘yan Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *