Mai Horas Da ‘Yan Wasan Kasar Libya Ya Ajiye Aikinsa

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta kasar Libya wato Faouzi Benzerti ya ajiye aikinsa amatsayinsa na mai horas da kungiyar kwallon kafa ta kasar bayan ya kwashe wasu watanni yana jagoranatar kasar ta Libiya dake nahiyar Afrika.

Ya ajiye aikin nasane bayan Kwantaraginsa ta kare daya sanya tun awatan Oktoba na shekarar 2019 inda ya shafe kimanin watanni shida yana jagoranatar kungiyar kwallon kafan ta kasar Libya.Saidai dukkanin tsawon watanni shidan dayayi yana jagoranatar kungiyar kwata-kwata wasanni biyu ya jagorancesu, wato wasan da kasar ta Libya tasha kashi ahannun kasar Tunisia daci 4 – 1, saikuma wasan da kasar ta Tunisia ta sami nasara ahannun kasar Tanzania daci 2 – 1

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *