Maganar Gaskiya, Ni Ba Faɗakarwa Na Ke Ba – Jarumi Ali Nuhu

Fitaccen Jurumin finafinan Hausa nan na Kannywood wanda ake cewa SARKI wato Ali Nuhu Muhammad ya ce shi ba fadakarwa ya ke ba, kuma bai taba cewa ya na fadakarwa ba. Jarimin ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan Radio Express Kano, ga yadda hirar ta gudana:

Tambaya: Daga karshen karshen 2019 har zuwa yanzu akwai wasu Fina-finai da kai ka ke bada Umurni zaa ga cewa akwai wasu kebantattun jarumai da kake sanyawa a Finafinanka irinsu Umar M. Sharif da Maryam Yahya da Hassana Muhd da sauransu, wasu suna cewa me yasa ba za ka baiwa wasu jaruman dama ba?

Ali Nuhu: Wato Abu daya da na sani shi ne tun da aka kafa masana’artar finafinan Hausa baa ta ba yin wani Darakta ba wanda yake Promoting din jarumai maza da mata ba kamar ni, idan kuma har zaa yi wannan korafin to akwai matsala kenan… domin akalla mata 12 zuwa 13 na yi promoting maza 9 zuwa 10 na yi promoting suka zama Jarumai. Sannan akan magana aiki kuma ya kamata mutane su gane ko a Fim din FKD ne idan ni Ali Nuhu bai dace da role din ba, ba za a saka shi ba, kwana nan nan na kallama wani sabon fim mai suna ‘Bana Bakwai’ ka ganni a ciki? Babu ni a ciki saboda babu role din da yi a ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *